Kimiyya

Infinix Sun Ƙaddamar Da “Note 30 Pro” Mai Saurin Caji

Infinix sun ƙaddamar da sabbin wayoyi a asirce da aka yiwa lakabi da Note 30, Note 30 5G, da Note 30 Pro. Wayoyin uku suna dauke da fasahar caji da sauri, suna yin caji cikin sauri kuma mai inganci akan caja da wireless charging.

Bari mu kalli yadda ɗaya daga cikin wadannan sabbin wayoyin take, wato Note 30 Pro.

Wannan wayar ta zo tare da babban sikirin mai kala mai kyau (AMOLED) tare da saurin aiki (120-Hz) da saurin taɓawa (Touching 360-Hz). Wayar tana da babbar kyamarar 108-MP ta baya da kyamarar selfie 32-MP ta gaba, kuma akwai fitila ta gaba domin daukar hoto cikin dare ko wurare masu duhu.

Infinix Note 30 Pro tana dauke fasahar da ke sanyaya wayar da yin zafi ko dumi, domin ba ku damar yin aiki da wayar na tsawon lokaci.

Haka zalika, Note 30 Pro waya ce mai dauke da LTE, domin shiga yanar gizo Internet cikin sauri, kuma tana caji akan 68W. Bugu da kari, Note 30 Pro za ta yin caji  zuwa 80% cikin mintuna 30 (kamar yanda aka tallata).

A karshe, Note 30 Pro ta zuwa da memori 128GB, 8GB RAM da 256GB, 8GB RAM wanda za’a iya karawa har zuwa 16GB RAM. Wayar tana dauke da Android 13, XOS 13 da batir 5000mAh.

Advertisement