Kimiyya

Labarin Wata Yarinya Mai Suna ‘Mangli’ Wacce Ta Auri Kare Saboda Al’ada

Labarin Mangli Munda labari ne mai sosa rai kuma yana nuna ikon al’adu da al’ada. Mangli wacce budurwa ce ta auri wani kare da ake kira Sheru a wani bikin aure mai kayatarwa wanda ya samu halartar mutane da yawa.

Mangli Munda, wacce ta ya fito daga gabashin Indiya ta samu labarin daga dattawan garin su cewa dole ne a dauki wannan al’ada domin a aurar da ita ga kare. A cewar dattawan yankin, yarinyar ta kasance cikin sihirin wani mummunan aljani wanda ya haifar mata da mummunan sa’a a rayuwa.

Idan yarinyar ta auri kowane mutum, to za ta kawo hallaka ga mutumin, dangin da sauran jama’ar gari saboda mummunan sihiri da ke tasiri cikin al’adar su.

Auren karen shine a matsayin tsafta ce yarinyar. An kawo kare a wurin bikin a cikin mota kuma an yi masa maraba da fara’a.

Ga iyayen Mangli sun aminta da auren kuma har mahaifinta ne ya gano ɓataccen kare kuma ya ga kare a matsayin mafi dacewa da ya auri Mangli.

Game da Mangli, ba ta son al’ada amma dole ne ta sha al’adar don amfanin kanta. Bayan sun auri karen, dattawan sun yi amannar cewa yarinyar za ta tsarkaka kuma har ma za ta iya yin aure ta hanyar da ta dace da mutum dan uwanta.

A cewar al’umar, wannan al’ada ce da ta zama ruwan dare a tsakanin membobin al’umma kuma ba ita ce ta farko ba.