Labarai

Gobara Ta Tashi A Gidan Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

Sassan gidan kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Hon. Bilyaminu Ismail Moriki ya kone da wuta a Gusau babban birnin jihar.

Lamarin ya faru ne a karshen mako.

Ba a samu asarar rayuka ba amma dukiyoyi na miliyoyin Naira sun lalace.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Shugaban Majalisar, Bello Madaro ya fitar, magatakardar Majalisar, Alhaji Mahmud Aliyu, ya bayyana kaduwarsa a madadin majalisar da ma’aikatanta, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban bala’i.

Ya kuma bayyana tashin gobarar a matsayin wani aiki da Allah ya kaddara, tare da jajantawa shugaban majalisar, da iyalansa, da al’ummar mazabarsa a yankin Zurmi ta yamma.

Tuni dai wasu jiga-jigan siyasa da masu fada aji sun ziyarci shugaban majalisar domin jajantawa.

Shugaban majalisar ya yi godiya ga Allah da ba a yi asarar rayuka ba, ya kuma gode wa duk wadanda suka taimaka wajen shawo kan gobarar.