Labarai

Isra’ila Tayi Ikirarin Kashe Shugaban Kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah

Sojojin Isra’ila sun ce sun kashe shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah a wani hari ta sama da suka kai a Beirut babban birnin kasar Lebanon, ko da yake kungiyar ba ta fitar da wata sanarwa kan makomarsa ba.

“Hassan Nasrallah ya mutu,” in ji kakakin soji Laftanar Kanar Nadav Shoshani a ranar Asabar. An kuma kashe Ali Karki, kwamandan yankin kudancin Hezbollah, da wasu karin kwamandojin Hezbollah a wani kazamin harin da jiragen yakin da aka kai a kudancin birnin Beirut da ke wajen Dahiyeh a ranar Juma’a, in ji rundunar sojin Isra’ila.

Ma’aikatar kula da lafiyar jama’a ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, mutane 6 ne suka mutu yayin da wasu 91 suka jikkata sakamakon harin bam din da ya rutsa da wasu gidaje shida. Hare-haren jiragen saman Isra’ila sun ci gaba da kaiwa yankunan kudancin birnin Beirut da sauran yankunan kasar Lebanon hari a ranar Asabar.

Yayin da kungiyar Hizbullah ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan Nasrallah ba, wata majiya na kusa da kungiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa tun ranar Juma’a ta yi batan dabo.

Nasrallah mai shekaru 64 a duniya ya shafe fiye da shekaru 32 yana jagorantar kungiyar da ke samun goyon bayan Iran, yana rike da mukamin jagora na siyasa da ruhi da ke jagorantar kungiyar Hizbullah zuwa wani wuri mai suna a Lebanon.