Kimiyya

Dattijo Dan Najeriya Mai Shekaru 67 Ya Ƙirkiri Risho Mai Aiki Da Ruwa

Hadi Usman dan shekara 67 baya bukatar iskar gas ko kananzir wajen samar da wuta don girki.

Jaridar PR Nigeria ya ruwaito cewa, masanin na’urorin lantarkin ya kirkiro sabbin fasahohin ne saboda burin shi na bayar da tallafin kudin amfani da iskar gas da kananzir.

Wani faifan bidiyo na YouTube ya nuna Hadi yana nuna yadda murhun da ake sawa ruwa ke haifar da wuta.

Mutumin mai hazaka wanda a baya ya hada na’urar watsa shirye-shiryen rediyo tare da gudanar da gidan rediyon al’umma yana son cibiyoyi masu dacewa su taimaka masa don samun haƙƙin ƙirar shi.