Tarihi

Dalilin Da Yasa Donetsk Da Luhansk Suka Zama Tushen Rikicin Rasha Da Yukiren

Fiye da mutane 14,000 ne aka kashe a fada tsakanin sojojin Ukraine da ‘yan awaren da ke samun goyon bayan kasar Rasha (Moscow) tun shekara ta 2014.

Jamhuriyar Donetsk da Luhansk da ke da’awar kasashen kan su, wadanda Moscow ta amince da yancin kan su a ranar Litinin, suna cikin tsaka-tsaki a gabashin Ukraine, kuma sun balle daga ikon kasar Ukraine a cikin 2014.

Tun daga wancan lokacin, fiye da mutane 14,000 aka kashe a fada tsakanin sojojin Ukraine da yan awaren da ke samun goyon bayan Moscow a can.

Game da yankin;

Donetsk, wandda ke kewaye da tarin tudu, shine babban birni a cikin kwarin ma’adinai na Donbas.

An taɓa sakawa yankin suna Stalino, babbar cibiyar masana’antu ce mai dauke ma’adinai.

Hakanan yana daya daga cikin manyan cibiyoyin samar da karafa na Ukraine.

Tana da mazauna miliyan 2.

Luhansk, tsohon Voroshilovgrad, kuma birni ne na masana’antu da ke da mazauna miliyan 1.5.

An haɗa su a cikin basin, a kan iyaka da Rasha a arewacin bankunan Bahar Maliya – gida ga tarin kwal.

Kasancewar masu magana da harshen Rashanci ya zo ne yayin da aka tura ma’aikatan Rasha da yawa zuwa wurin bayan yakin duniya na biyu a lokacin Soviet.

Rikici tun 2014;

Yankunan sun kasance cikin rikici da sojojin Ukraine tun bayan wani bore da ke samun goyon bayan Kremlin biyo bayan mamaye yankin Crimea da Rasha ta yi a shekarar 2014.

Kasashen duniya ba su amince da yancin kan su ba, wanda aka shelanta bayan kuri’ar raba gardama.

Ukraine da kasashen Yamma sun ce Rasha ce ta tayar da boren gabashin kasar, inda ta zuba makamai da sojoji a kan iyakar kasar domin karfafa su.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya fada a ranar Litinin cewa ya amince da yancin kan Donetsk da Luhansk.

Har ila yau Donbas tana cikin tsakiyar yakin al’adu tsakanin Ukraine (Kyiv) da Rasha (Moscow), wanda yace yankin, wani yanki mai girma na gabashin Ukraine, yana magana da yaren Rasha kuma yana buƙatar kariya daga kishin kasa na Ukraine.

Yarjejeniyar zaman lafiya;

Kokarin warware rikicin gabashin Ukraine, da aka shimfida a yarjejeniyoyin Minsk na shekarar 2015, ya ci tura. Kyiv da yan awaren kowanne ya zargi juna da keta dokoki.

An dai samu jerin tsagaita wutar da aka yi a kasar sakamakon keta haddin da yan tawaye ke yi.

Bangaren siyasa na yarjejeniyoyin, wanda ke hasashen samun yancin cin gashin kai ga yankunan yan tawaye da kuma zabukan kananan hukumomi a karkashin dokokin Ukraine, ya kasance ajalinsu, inda kowanne bangare ke zargin daya da gazawa.