Nishaɗi

Bintu Dadinkowa, Jarumar KannyWood Ta Rasu

Daga Allah muke, kuma a gare mu masu komawa ne!

Allah ya yiwa jarumar KannyWood, Bintu Dadinkowa rasuwa.

Jarumar KannyWood da take fitowa a matsayin Bintu ta shirin Dadinkowa na tashar Arewa 24 ta rasu ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu, 2024.

Mun labarin cewa jarumar ta rasu sakamakon gajeruwar rashin lafiya da tayi fama da ita.

Allah Ya gafarta mata.