Bayan Janye Takunkumin ECOWAS, Nijar Ta Rufe Iyakarta Da Benin

Takunkumin kungiyar kasashen yammacin Afirka, ECOWAS kan jamhuriyar Nijar an janye shi a ranar Asabar din makon da ya gabata, bayan wani taron gaggawa na kungiyar a birnin Abuja, Najeriya.

Takunkumin da aka sanyawa Nijar bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023. Watanni fiye da 6 da suka wuce, iyakoki tsakanin Nijar da Benin sun kasance rufe.

Sai dai kuma, a yanzu, hukumomin Cotonou sun bude iyakar su da Nijar, yayin da a bangaren Nijar iyakar ta kasance a rufe.