Labarai

Bama Tsoron Mutuwa: Bello Turji Ya Kalubalanci Gwamnati A Cikin Wani Sabon Bidiyo Da Ya Saki

Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji ya ce shi da abokansa ba sa tsoron mutuwa.

Turji ya ce shi da sojojin sa ba za su dauki makami ba idan da suna tsoron mutuwa.

Shugaban ‘yan bindigar ya bayyana hakan ne a cikin sabon faifan bidiyonsa inda ya yi barazana ga gwamnati kan yadda za ta tura shugabannin ma’aikatar tsaro jihar Sokoto domin yakar kungiyarsa.

A cikin faifan bidiyon da ke yawo a yanar gizo, Turji ya ce: “Idan da suna tsoron mutuwa, da ba za mu dauki makami ba tun da farko, ku daina tura shugabannin tsaro a bayan mu.”

A kwanakin baya ne wasu faifan bidiyo suka bayyana a yanar gizo na Turji da yaransa suna murna bayan sun kwace wasu motoci biyu na Mine Resistant Ambush Protected Vehicles, MRAP, mallakar sojojin Najeriya.

Amma Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, DHQ, ta yi watsi da ikirarin Turji na kwace MRAPs guda biyu.

DHQ ta ce an bar motocin MRAP guda biyu ne saboda gazawar da sojoji suka yi wajen zakulo su bayan sun makale a wani wuri mai fadama a lokacin da suke kai farmaki kan ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

A ranar Talatar da ta gabata ne Ministan Tsaro, Shugaban Hafsan Soji, CDS, Janar Christopher Musa da wasu manyan hafsoshin soji suka kai farmaki jihar Sakkwato a lokacin da suke bayyana shirinsu na jagorantar farmakin da sojoji suka kai wa Turji da sauran ‘yan bindiga, masu aikata miyagun laifuka a yankin Arewa maso Yamma.