An Daure Wani Mutum Shekara 50 A Gidan Yari Bisa Laifi Sakawa Matar Shi Barkono Da Sufa Gulu A Farji

Wani mutum mai suna James Kifo wanda ya rufe al’aurar matar shi da wani super glue an daure shi shekaru 50 a gidan yari.

Kotun Chuka ta yankewa James Kifo Muriuki hukuncin; wani mutum da ya mutuncin matar shi, daurin shekaru 50 a gidan yari. Hakan ya biyo bayan hukuncin da aka yanke masa na lalata da matar shi.

Kifo ya jagoranci matar shi zuwa kogin Kathita da ke Marimanti da daddare, inda ya bukace ta da ta tube tsirara kuma ta bayyana masa duk mutanen da ta kwana da su lokacin da ya tafi Nairobi.

Kifo ya cigaba da dukanvta kafin ya yayyafa mata barkono da gishiri da super glue a farji din ta. Daga nan sai ya tura su cikin al’aurar ta da wuka.

Wata tawagar ‘yan daba ta DCI daga sashin kula da manyan laifuka na musamman, DCI Tseikuru da DCI Tharaka South Sub County ne suka kama Kifo a maboyar shi da ke Kaningo a gundumar Kitui. Yana boye a gidan James Murogi.

Tun daga wannan lokacin, Kifo ya ci gaba da cewa bai aikata laifin ba.