Al'umma

Yarinya Yar Shekara 13 Da Ta Bada Amsar Tambayoyin Lissafi 34 Cikin Sakan 172

hazikar matashiyar Najeriya, Nasara James Dabo ta samu damar zuwa fagen gasar duniya tare da kwazon ta a fannin lissafi (Math).

A cikin gasar lissafin da aka kammala na International Mathematical Olympiad training (IMO), wata matashiya yar shekara 13, Nasara James Dabo, dalibar makarantar Ideal international college, Kaduna, haifaffar Kaduna, ta kai ga matsayin daya daga cikin matasa a wajen gasar.

Matashiyar wan’dda ta halarci gasar Olympiad ta Duniya (IMO) ta kammala gasar tana da maki 145 jimla, inda ya warware tambayoyin Lissafi 34 a cikin dakika (second 172), ma’ana (kasa da mintuna 3).