Al'umma

Yanzu Sam Ban Jin Dadin Rayuwa, Ina Fatan Cikawa Da Imani – Dantata

Dantata, mai shekaru 91, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima.

Ya ce tun yana matashi yana da damar haduwa da mutane da dama kuma ya kulla abota a duk jihohin Najeriya amma da kyar ya iya kiran mutum 10 da ke raye.

“Na zagaya duk jihohin Najeriya kuma na yi abubuwa da mutane a duk jihohin, da yawa abokai ne amma abin bakin ciki, duk mutanen da na sani, da kyar na iya kiran mutum 10 da ke raye.

“Gaskiya, kamar yadda nake a yanzu, ina jira kawai lokaci na. Ban jin daɗin rayuwa ba yanzu. Ina fatan in bar duniya da imani.