Wasanni

Yanda Sergio Aguero Ya Auri Yar Maradona, Sunil Chhetri Ya Auri Yar Subrata

Diego Maradona ya jagoranci tawagar kasar Argentina daga 2008 zuwa 2010 kuma Sergio Aguero ya taka leda a karkashin shi. A cikin 2008, Aguero ya auri ƴar shi Gianinna Maradona.

Aguero ya lashe gasar Premier, FA Cup, Europa League, UEFA Super League, Copa America da dai sauransu. Haka kuma shi ne wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a tarihin Man City kuma kwanan nan aka shigar da shi babban dakin taro na Premier League.

Dan wasan gaba na Indiya Sunil Chhetri ya taka leda a karkashin Subrata Bhattacharya a Mohun Bagan. Daga baya ya auri diyarsa Sonam Bhattacharya.

Chhetri ya lashe gasar Super League ta Indiya, da I-League, da gasar Indian Federation Cup, da AFC Challenge Cup, da dai sauransu, kuma yana daya daga cikin wadanda suka fi zura kwallo a raga a fagen kwallon kafa na duniya da yawan kwallaye 70.

Darasi: Idan kana son samun nasara sosai, ka auri yar kocin ka.