Wasanni
Yadda Najeriya Tazo Ta 3 A Gasar AFCON Har Sau (3) A Jere
Najeriya ta zo na uku a gasar AFCON sau uku a jere.
A shekara ta 2002, sun yi rashin nasara a hannun Senegal da ci 2-1 bayan karin lokaci a wasan kusa da na karshe, sannan kuma ta doke Mali da ci 1-0 a wasan na uku.
A shekara ta 2004, sun yi rashin nasara da ci 5-3 a bugun fanariti a hannun Tunisia a wasan dab da na kusa da na karshe, sannan ta doke Mali da ci 2-1 a matsayi na uku. Sai dai har yanzu dan wasan Najeriya Austin Okocha ya kare a matsayin wanda ya fi kowa zura kwallaye a gasar.
A shekara ta 2006, ta sha kashi a hannun Ivory Coast da ci 1-0 a wasan kusa da na karshe, sannan ta doke Senegal da ci 1-0 a wasan na uku.