Al'umma

Yadda Bello Turji Kachalla Zama Sabon Sarkin Gobir

A makon da ya gabata shugabannin kungiyar ci gaban al’ummar Gobir (GCDA) sun koka kan halin da kasar su ta shiga, an kasa yin wani taimako, sai ans mamakin yadda yankin da ya kasance mafi karfi a kasar Hausa tun kafin mulkin mallaka, ya fi karfin fada a ji a yanzu, ya shiga tsaka mai wuya sanadin hare-haren ƴan bindiga.

Wannan yanki da ya wanzu tsawon shekaru 800 yayin da babban birnin Gobir ya hade a cikin Daular Sakkwato bayan rasuwar Sarkin Gobir Yunfa da faduwar babban birninsa, Alkalawa a 1808.

Kananan hukumomin Sabon Birni, Goronyo, Isa da sauransu a jihar Sokoto da kuma karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara yanzu haka suna karkashin ikon wani hatsabibin maras imani mai Bello Turji Kachalla.

Ɗan ta’adda Turji yana yin garkuwa da fyade yadda ya ga dama. Yakan toshe titina, yana watse kasuwa, yana kwace abinci da duk wani abu da yake so, kuma yana kashe duk wanda ya ki. Ya kori sarakunan kauye sannan ya nada nasa hakiman kauye.

Turji yana karbar haraji daga al’umma, duk wani kauye da ya kasa biyan haraji, Turji yakan ziyarce shi da farmakin gaggawa ba tare da jin kai ba, yana kashe duk wanda ya samu ciki har da mata da yara.

Daga cikin kauyukan da Turji ya tarwatse akwai Gajit, Lajinge, Tarah, Unguwar Lalle, Kurawa, Gangara da Garin Idi. A wata daya da ya gabata Bello Turji ya watse kauyen Garki mai tazarar kilomita biyar daga Sabon Birni tare da kashe mutane 80 a dare daya.

A ranar Talatar makon da ya gabata, wannan dan ta’adda ya aiwatar da daya daga cikin munanan aikin shi, inda yan ta’addan shi suka tare wata motar bas da ta taso daga Sabon Birni, inda suka banka mata wuta tare da kona aƙalla mutum 23 da ran su. Mutanen sa sun tsaya gadi a kusa da motar bas yayin da mutane ke konewa suna zama gawayi.

A karkashin mulkin Bello Turji, GCDA ta ce “babu noma, babu tafiye-tafiye babu kasuwa” a yankin. Shugaban kungiyar ya kara da cewa “Babban matsalar da suke fuskanta a yau ita ce kana cikin gidanka ‘yan ta’adda sun zo suna cin zarafinka a gaban iyalinka. Kuma duk al’ummar da na gaya muku ana biyansu haraji, kuma sun biya. Amma ko da sun biya, ba su samu kwanciyar hankali ba.”

A lokacin da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya karbi tawagar binciken gaskiya ta manyan jami’an tsaro da na leken asiri na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno a Sokoto a ranar Juma’ar da ta gabata, ya tabbatar da cewa an mika wani bangare na mulkin jihar Sakkwato ga Bello Turji.

Tambuwal ya ce, “sassan jihar nan na cikin mummunan yanayi na ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, tare da tada zaune tsaye da kuma tsorata jama’a a ‘yan kwanakin nan.” Ya ce yanzu haka ana kai hare-hare da garkuwa da mutane da rana a wasu sassan Isa, Sabon Birni, Tangaza. Illela da sauran kananan hukumomi da dama.”

Ga alama GCDA ta yi magana ne a kan yankin da ta damu, Gobir, amma sauran yankunan da ba na Gobir ba, su ma suna karkashin takalmin ‘yan ta’adda ne.

Duk da cewa wasu sassa na jihar Sokoto sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga shekaru da dama, Gwamna Aminu Tambuwal ya shaida wa tawagar gwamnatin tarayya a ranar Juma’a cewa “wannan lamarin ya kara ta’azzara sakamakon kwararowar ‘yan fashi da masu aikata miyagun laifuka daga muhallansu sakamakon hare-haren jami’an tsaro da aka tura a karkashin Operation Hadarin Daji a makwabciyar jihar Zamfara.”

Tambuwal an kaddamar da Operation Hadarin Daji a Zamfara ba tare da wani katabus ba a jihar Sokoto.”