Yadda Ƙasar Algeriya Ta Yi Wasanni Masu Ban Mamaki A Gasar Cin Kofin Duniya Ta 1982
Algeria ta fara buga gasar cin kofin duniya a shekarar 1982, inda ta samu kanta a rukunin ‘C’ da Jamus ta Yamma, da Ostiriya da kuma Chile.
Abin da ya ba mutane mamaki mamaki shi ne, sun lallasa Jamus ta Yamma da ci 2-1, Ostiriya kashi hannun su da ci 2-0, sannan ta doke Chile da ci 3-2.
Wasan karshe a wannan rukuni ya kasance tsakanin Jamus ta Yamma da Ostiriya. Kafin wannan wasan na karshe, Algeria da Ostiriya dukkansu suna da maki 4, bayan da suka yi nasara a wasanni 2 kowanne (nasara ita ce maki 2 a baya), yayin da Jamus ke da maki 2. Nasarar da ci daya ko biyu ga Jamus ta Yamma, zai sa dukkannin Jamus ta Yamma da Ostiriya su samu tikitin shiga gasar da maki, inda Algeria ta sha kashi.
Jamus ta Yamma ta zura kwallo a raga cikin mintuna 10, sai dai ba a yi wani gagarumin yunkurin zura kwallo a raga ba a sauran mintuna 80 da suka rage. An yi imanin cewa kungiyoyin biyu sun amince a bar wasan a kare a haka, domin dukkansu za su samu tikitin shiga gasar. Babu shakka da yawa daga cikin ‘yan kallo ba su ji daɗi ba, domin an yi ta rera waƙoƙin nuna rashin amincewa kuma magoya bayan Aljeriya sun yi wa ‘yan wasan hannu da takardar kuɗi, wanda ke nuna cewa an sayar da wasan.
An tashi wasan da ci 1-0 kuma an fitar da Aljeriya. An zargi kungiyoyin biyu da karkatar da wasa amma FIFA ba ta gamsu sosai ba. An san wannan wasan da ‘Abin kunya na Gijon.’
Sai dai wannan lamarin, haɗe da wasu irin wannan lamari, ya sa FIFA ta yanke shawara cewa daga baya za a buga wasanni biyu na ƙarshe a kowace rukuni a lokaci guda.