Addini

Matasa Kiristoci Sun Saya Wa Masallacin Juma’a Engine Generator A Filato

Wasu matasa Kiristoci masu kishin kasa sun saya wa masallacin juma’a sabon ‘Engine Generator’ a jihar Filato.

An habarto cewa, matasan sun fito ne daga garin Gana Ropp da ke karamar hukumar Barikin Ladi.

Wani rahoto ya nuna cewa masallacin yana fuskantar kalubale da dama sakamakon karancin haske a cikin watan Ramadan.

Jami’an masallacin sai sun aro Engine Generator daga wani masallaci kafin su gudanar da tafsirin ramadan da sallar Juma’a.

A lokacin da yake karbar Engine ɗin, babban limamin, Uztas Muhammad Ahmad yayi godiya tare da yaba wa samarin bisa wannan karimcin da suka nuna.

Malam Ahmad yayi kira ga yan uwa musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’un su, ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummomin mu daban-daban.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya cigaba da yi masu albarka, ya kuma saka musu da yawa a kan ayyukan da suke yi wa bil’adama.