Al'umma

Wani Mutum Ya Fusata, Ya Hukunta Bera Saboda Cin Sabbin Kudin Shi [HOTUNA]

Wani matashin dan Najeriya ya shiga shafukan sada zumunta inda ya koka kan yadda aka lalata masa sabbin takardun kudin Naira da ya mallaka.

Ya bayyana cewa bera ya ci wani kaso na sabon kudin da ya ajiye a wani sashe na gidansa sakamakon karancin naira a kasar.

Mutumin ya fusata sosai, ya ladabtar da bera saboda cin sabuwar takardar kudin Nairar shi.