Addini

Wa’azi Kan Aƙida A Jihar Kano

Ina ganin da dama daga cikin yan uwa suna cewa malumman Sunnah na jihar kano basu cika wa’azin aqida ba, kuma basu yakar akidar Tijjaniya, wato suna neman yardan yan bid’a.

Nace sakin wannan maganar ba tare da kaidi ba zalunci ne da rashin adalci. Kuma ina yiwa masu wannan maganar uzuri saboda galibin su basu bibiyar karatuttukan irin su Dr. Muhammad Umar Sani Jijiyar Lemo.

Kuje Ku saurari karatun littafin الفرقان بين الحق والبطلان na Ibn taimiya Rahimahullah, wanda Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya karantar, da sauran littafafai kuji yadda Mallam yake warware shubuhohin yan bid’a a ilmance wanda almajirai na ilimi muke samun anfani sosai domin Mallam yana karantar damu yanda ake warware shubuhohin yan bid’a.

Shin kun karanta littafin da Dr Muhammad Umar Sani Rijiyar Lemo ya rubuta mai suna?
هذه هي الفيضة إنياس وآراؤه في الميزان.

Galibi mu almajirai wannan zamani muna da kiwuya sosai wurin karatun littafi, amma mun fi gane sauraran bidiyo da murya, wata audio, saboda haka, bamu san kimar wannan littafin ba. Da ace duk wani Ahlusunnah Ghana, Nijar da Nageria zai karanta wannan littafi na Mallam Muhammad Umar Sani Rijiyar Lemo, da zai taimaka masa sosai wurin rusa akidun bid’a da zai yi wuya sosai yace Mallam Muhammad Umar Sani yana mujamala a akida amma masalan mu, shine baza mu karanta ba.

Mallam yana cikin na gaba-gaba a sahun wadannda suka rusa akidun bid’a ilmance, kuma duk wanda ya karanta wannan littafin na tabbata zai yi shedar hakan, saboda haka kuskure ne ka yanke wa mutumin da baka bibiyar karatuttukan sa hukunci da cewa baya rusa akidun bid’a, domin wannan littafin هذه هي الفيضة babban kundi ne da marja’i na duk Ahlusunnah wurin rusa akidun bid’a domin idan ka karanta littafin zaka samu duk abinda kake bukata wurin rusa akidun bid’a da dalilai masu karfi.

Wanda wannan littafin ya tada hankalin yan bidi’a sosai, masu cin mutuncin Mallam suna yi masu raddi sunayi, har littafafai aka rubuta na cin mutuncin Mallam Muhammad Umar Sani Rijiyar Lemo akan wannan littafin da ya rubuta kowa shaida ne akan hakan, masu karyan salafiyya shuru sukayi, babu wanda yazo kare wannan littafin, ballantana Mallam, duk da littafin akida ne, saboda kiyayyar su ga Mallam, amma na tabbata da malamin su ya rubuta littafin kuma yan bid’a suka kawo masa hujumi da munji su ta ko wani soko da lungu suna raddi, Allah ya rabamu da son zuciya, amma a haka kuma ace Mallam na mujamala a akida?

Kace kawai baka son usulubin sa, amma karya kake yi kace baya raddi wa yan bid’a, kuma zancen usulubi kuma kowa da yanda Allah ya yisa wani baida zafi wani kuma yana da zafi cikin komai, haka Allah yake halittan sa, wani gajere wani dogo, wani baki wani fari, saboda haka ni ina son dukkanin su, mai zafi da mara zafi matukar dukkanin su suna rusa akidun yan bid’a.

A karshe, duk wani malami daga cikin malumman mu na Sunnah muna girmama shi kuma muna addu’a Allah ya gafarta wa malumman kurakurai su inda suka yi dai-dai, Kuma Allah ya basu lada.


الإمام الشافعي