Wasanni

Tarihin Ɗan Wasan Uruguay, Sebastian Abreu Da Ya Bugawa Kulob 32 Wasa A Kasashe 11

Tsohon dan wasan kasar Uruguay Sebastian Abreu ya buga wasa a kungiyoyi daban-daban 32 a kasashe 11 kuma ya rike mafi yawan kungiyoyin da ya taba bugawa a tarihin kwallon kafa.

Dan shekaru 45 ya yi ritaya daga buga kwallon kafa a watan Yunin 2021 amma a takaice ya fito daga ritaya ya buga wa kulob din garinsa Olimpia de Minas wasa.

A matakin kasa da kasa, ya buga wa Uruguay wasanni 70 ya kuma ci kwallaye 26.