Tarihin Aminu S Bono, Daraktan Fina-Finai A KannyWood
Kaɗan daga cikin tarihin rayuwar Aminu S Bono, fitataccen daraktan a masana’antar fina-finai ta KannyWood da ke Arewacin Najeriya.
Aminu S Bono an haife shi a 15 ga watan June, shekara ta 1982; kawo yanzu yana shekaru 41 a duniya.
S Bono mabiyin addinin ɗarikar Qadiriyya ne, wacce ke da ɗin mabiya a jihar Kano da sauran jihohin a Arewacin Najeriya da ma Afrika baki ɗaya.
S Bono jarumi ne kuma darakta a harkár fina-finan Hausa. Yayi bada umarni a fina-finai masu yawa, kamar fim din “Mai Numfashi” a shekarar (2017), “Bazura Sudan” a shekarar (2018), da “So Haduwar Jini” a shekarar (2019)”.
S Bono yana da kyakkyawar alaƙa da sauran jarumai da daraktoci maza da mata a masana’antar fina-finai ta KannyWood.
Sai dai Allah ya yiwa jarumin kuma darakta rasuwa a ranar (20 ga Nuwamba, 2023).