Al'umma

Talauci Na Daga Cin Abinda Ya Kawo Mutuwar Mutane Da Yawa A Fashewar Tankar Mai A Jigawa

Da yake zantawa da Al Jazeera, wani mazaunin yankin da tankar mai ta fashe a jihar Jihar, Adamu Lawan ya ce shi da wasu mutane uku suna zaune a bakin titi kusa da kofar makarantar Adams Science Tahfizul Quran Academy da ke da tazarar mita 15 daga wurin da hatsarin ya afku, sai suka ga motar ta karkace ta kife a daren ranar Talata, lamarin yqyi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 170 kawo yanzu.

“Man fetur dake cikin tankar ya zube a cikin magudanar ruwa kuma mutane sun fito gaba daya domin su debo,” in ji shi, sai ta fashe da gobara.

Lawan ya ce karuwar matsalolin tattalin arziki “wani bangare” ne ke da alhakin mutanen da ke yin kasada don tattara man da ya zube. Ba haka mutanen garin za suke yi ba idan irin wannan hadurran da motocin man fetur suka yi a baya ba, in ji shi. “Amma yanzu mutane suna fuskantar wahala kuma suna neman duk wata hanya ta samun sauki,” in ji shi.

Wani wanda hatsarin tankar ya shafa

Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da tabarbarewar tattalin arziki, inda man fetur ya zama wani abu mai daraja da tsada ga mutane da dama. Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi tun lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki a watan Mayun da ya gabata ya kuma janye tallafin man fetur, inda ya tashi daga kimanin naira 175 ($0.1) a lita daya zuwa sama da naira 1,000 ($0.6).

A sa’i daya kuma, hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya sama da kashi 30 cikin dari na tsawon watanni, inda ya kai kusan shekaru uku da ya kai kashi 34.19 cikin dari a watan Yuni kafin ya ragu kadan zuwa kashi 32.7 a watan Satumba, 2024.

A cewar Bankin Duniya, kashi 56 cikin 100 na ‘yan Najeriya na rayuwa ne kasa da kangin talauci.