Siyasa

Taƙaitaccen tarihin hamɓararren shugaban ƙasar Burkina Faso Christian Kabore

Jaridun Burkina Faso ɗauke da hoton Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda ya dare mulki bayan hambarar da Roch Marc Christian Kabore.

An zabi dan shekaru 64 a duniya a shekara ta 2015 bayan wata zanga-zangar da ta tilasta wa Blaise Compaore sauka daga mulki.

An sake zabe shi a shekarar 2020. Amma tun a shekarar da ta gabata, ya fuskanci tashin hankali game da hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai da suka kashe mutane kusan 2,000 tare da tilastawa miliyan ɗaya da rabi barin gidajensu.

A ranar Lahadin da ta gabata, hare-haren bindigogi da kashe-kashe ya ɓarke a wasu barikokin soji kwana guda bayan yan sanda sun tarwatsa haramcin zanga-zangar, kuma a ranar litinin, yan tawayen sojojin sun maida ƙasar ƙarƙashin ikon ƙungiyar Patriotic Movement for Preservation and Restoration (MPSR), gwamnatin soja karkashin jagorancin Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba.

Advertisement

MPSR ta sanar da dakatar da kundin tsarin mulki tare da rusa gwamnati da majalisa inda Damiba ya fada a ranar Litinin cewa zasu yanke shawarar komawa ga tsarin mulkin “a cikin lokacin da ya dace”.

ECOWAS ta fada a ranar Litinin cewa, an tilasta wa Kabore yin murabus ne bisa barazana da kuma tursasawa.

Afirka ta Yamma ta fuskanci juyin mulkin soji uku cikin kasa da watanni 19, daga Mali a shekarar 2020 da Guinea a watan Satumban 2021.

Advertisement