Al'umma

Alu Wamakko Ya Tallafawa Jarirai 3 Da Kayan Masarufi Wadanda Mahaifiyar Su Ta Rasu

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya mai wakiltar Sakkwato ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ya tallafawa iyalan wani bawan Allah mai suna Sanusi Bello Gidan Salanke wanda mai dakin shi ta haifi yan uku (3) dukkan su maza da Mahaifiyar su ta rasu bayan kwanaki kimaanin bakwai (7) da haihuwa.

Sanata Wamakko ya bada wannan tallafin ne biyo bayan neman taimako da iyayen jariran yayi a wurin Sanata Wamakko.

Sanata Wamakmo da farko sanya aka sayawa jariran katifu barci 3, madarar jarirai irin wacce ake bayar wa ga yaron bai samun nonon uwa ba, kayan sakawa, mayukan shafawa da kayan wanka da wanki na jarirai, da suaran dukkanin abubuwa da jarirai suke bukata na rayuwa.

Sanata Wamamko bai tsaya a nan ba, ya sanya aka sayawa masu kula da jariran tunda ba babu mahaifiyar su buhun shinkafa gumi da dukkan sauran kayan abinci da kuma wasu yan kudade koda wata lalura zata iya tasowa.

Da yake magantawa, a madadin mahaifin jariran, magajin mahaifin yaran 3, mai suna Muhammad Bello Gidan Salanke, ya bayyana jin dadin sa bisa irin karamcin da Sanata Wamakko ya yiwa dan uwan shi.

Ya kara da cewa hakika Sanata Wamakko ya mutum ne mai son taimakon jama’a, inda yace wannan tallafi da suka samu game da jariran, yazo bayan kwana 3 da gabatar da korafin su ga Sanatan.

Daga karshe sun roki Allah da ya sanyawa Sanata Wamakko albarka, kuma Allah ya shige masa gaba.

Advertisement