Labarai

Mutanen Da Suka Mutu A Fashewar Tanka A Jigawa Ya Kai 181, Mutum 80 Na Cikin Mawuyacin Hali

Gwamnan jihar Jigawa Umah Namadi ya bayyana adadin mutanen da suka mutu a fashewar tankar dakon man fetur a jihar zuwa 181, yayin da wasu 80 ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.

Namadi wanda ya kasance a fadar shugaban kasa a ranar Talata don yiwa shugaban kasa Bola Tinubu bayanin halin da ake ciki, ya bayyana cewa adadin da gobarar ya shafa iyalai 210.

Idan za a iya tunawa, lamarin ya faru ne a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, inda wata motar dakon mai, ta tashi daga Kano zuwa Nguru a jihar Yobe, ta fashe a Majia, dake karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa.

Lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 tare da raunata wasu da dama da ke diban mai kai tsaye.

Gwamnan ya ce tuni jihar ta kafa wani kwamiti mai karfi a karkashin jagorancin wani DIG mai ritaya domin binciki musabbabin faruwar lamarin sannan kuma ya shawarci gwamnati kan abin da za ta yi.

Da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin jihar, Namadi ya ce, “A halin da ake ciki a yau shi ne muna da mutane kusan 181 da suka mutu, kuma kimanin mutane 80 a asibiti da kuma kimanin iyalai 210 da lamarin ya shafa.

“Na zo nan ne domin in yi wa shugaban kasa bayanin abin da ya faru da mu, mummunan lamarin da ya faru a Jihar Jigawa wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

“Mun ga yana da muhimmanci mu zo mu yi wa shugaban kasa bayanin abubuwan da muke yi a matsayin gwamnati sannan kuma mu gode masa da ya aiko da tawaga nan take da lamarin ya faru.

“Tabbas, gwamnatin jihar ta dauki lissafin likitocin duk wadanda abin ya shafa. Mun yi wa iyalai da yawa dauki, don tabbatar da cewa sun ci gaba da rayuwa, haka kuma Mista Shugaban ya yi alkawarin shiga tsakani da kuma taimaka wa wadanda abin ya shafa.

“Ya kamata ku kuma tuna cewa shugaban kasa ya ba da umarnin gaggawa ga Corps Marshal cewa ya binciki wannan lamari, kuma ya samar da mafita ta dindindin ga wannan matsala a kasar.”