Labarai

Mutane Sama Da 90 Sun Mutu, Gommai Sun Samu Raunuka A Fashewar Tankar Mai Jigawa

Akalla mutane 90 ne aka tabbatar da mutuwarsu, wasu gommai suka samu raunuka sakamakon fashewar wata tankar mai a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa a ranar Talata.

Mista Shi’isu Adam, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da NAN a ranar Laraba.

Ya kuma ce an kwantar da wasu mutane 50 a asibiti sakamakon raunukan da suka samu sakamakon fashewar.

“Da misalin karfe 11:30 na daren ranar Talata a garin Majia da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, direban tanka ya rasa yadda zai yi a kusa da jami’ar Khadija inda ta fashe.

“Direban ya bar Kano ya nufi Nguru a Yobe lokacin da hatsarin ya afku,” in ji Adam.

Ya ce: “Mun damu cewa duk da gargadin da ‘yan sanda ke yi wa mutane da su kaucewa faruwar hadurran da suka shafi tankunan mai, har yanzu suna aikata irin wadannan abubuwa.

“Mutane sun taru a kusa da wurin da hatsarin ya faru, shi ne dalilin da ya sa aka samu asarar rayuka”.

Kakakin ya ce za a yi jana’izar mutanen da suka mutu da misalin karfe 9 na safiyar Laraba.

Ya kara da cewa wadanda suka jikkata na samun kulawa a babban asibitin Ringim.