Labarai

Mutane Sama Da 100 Da Gobarar Tanka Ta Kashe A Jigawa An Binne Su A Kabari Guda

An yi jana’izar mutanen da fashewar tankar man fetur ta yi a garin Majia na jihar Jigawa a wani babban kabari.

A daren ranar Talata ne wata motar dakon mai da ke jigilar man fetur ta fadi, kuma ta fashe, lamarin da ya yi barna a jihar Jigawa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Shi’isu Adam, ya ce direban tankar na kan hanyarsa ne daga Kano zuwa Nguru a Jihar Yobe lokacin da hadarin ya afku a kusa da Jami’ar Khadija da ke cikin Garin Majiya.

Adam ya bayyana cewa da misalin karfe 11:30 na dare direban tankar ya rasa iko da motar lamarin da ya yi sanadin wata mummunar fashewar da ta rutsa da mutane da dama a wurin.

Sai dai wani mai amfani da X mai suna @ImranMuhdz ya saka hoton kabari na marigayan tare da taken: “An yi jana’izar sama da mutane 100 da fashewar tanka ta shafa a garin Majia na jihar Jigawa.”