Al'umma
Muslunci: Labarin Kiristoci Biyu, ‘Isaac Da Jacob’ Da Suka Ɓace A Sahara
Isaac da Jacob yahudawa biyu ne da suka ɓace a Sahara.
A gajiye da kishirwa da yunwa suka iso wani kauyen musulmi.
Isaac ya ce wa Jacob: “Dole ne mu yi kamar cewa mu Musulmi ne don su ba mu abinci.
Jacob ya ce: “Ba zan yi ƙarya ba, zan faɗa musu gaskiya.
Da shigar su kauyen sai mutanen kauyen suka tambayi sunayen su.
Isaac ya ce sunana Abdallah, sai Jacob ya ce: Ni suna na Jacob.
Shugaban ƙauyen ya ce: Ku ɗauki ɗan’uwa Jacob a ba shi abinci da abin sha.
Sannan ya dubi Isaac yana cewa: dan’uwa Abdallah musulmi ne kuma Ramadana ne yanzu, don haka ku sama masa wurin hutawa har zuwa lokacin buda baki (fadi) ya sha ya ci.
#Afirka #Barkwanci