Al'umma

Musa Hassaji: Magidanci Mai Shekaru 67, Mata 10, Ƴaƴa 98 Da Jikoki 568

Musa Hassaji, mai shekaru 67, wanda za a iya kwatanta shi a matsayin uban kasashe da yawa idan har za a iya misaltawa da yawan yaran da ya haifa.

Musa Hassaji dan kasar Uganda, ba magidanci ne kawai ga mata 10 ba, har ga uban yara 98 abin alfahari. Bugu da kari, mutumin mai shekaru 69 yana da jikoki akalla 598.

Ana zargin dangin Musa su ne mafi yawa a kasar shi ta Uganda kuma mai yiwuwa a fadin yankin gabashin Afirka. Yana da ‘ya’ya 98 da mata 10, hakan na iya nufin cewa matan shi sun haifi ‘ya’ya akalla tara.

Rahotanni sun bayyana cewa, Musa Hassaji ya auri matar shi ta farko yana da shekaru 17 a duniya yayin da yake kan hanyar shi ta komawa makarantar sakandare.

Rahotanni sun bayyana cewa Musa Hassaji yana da gida daya da dukkan matan shi, kuma a cikin wannan babban fili ya gina wasu kananan gidaje na ‘ya’yan ahi daban.

Daga cikin ‘ya’yan shi sun hada da manya da suka riga sun yi aure yayin da kananan yara ke cigaba da karatu. Musa yace cikin sauki zai iya bambance yaran amma bai san duk sunayen su ba.

Musa dai haifaffen ‘ya’ya biyu ne inda suka yi ta faman samun rayuwa amma abin mamaki ya auri mata 10 sannan ya haifi ‘ya’ya 98.

Rahotanni sun bayyana cewa Musa ya daina karatun shi a matakin Standard Six amma daga baya ya samu damar juya dukiyar shi bayan ya shiga kasuwanci.

Matar Musa mafi ƙanƙanta ita ce, Kakazi za a iya cewa a matsayin ɗan shi domin tana da karancin shekaru fiye da wasu jikokin shi
98

A cikin faifan bidiyon, Musa yayi alfahari yana cewa, “Na yi arziki sosai, duk dangin da na buga kofar shi na nemi a ba ni amarya nan take ake ba ni.