Wasanni

Manuel Junior: Shahararren Ɗan Ƙwallon Ƙafa Na Ghana

Manuel “Junior” Agogo kwararren dan wasan kwallon kafa ne dan kasar Ghana, wanda ya taka leda a matsayin dan wasan gaba.

A matakin kulob din, ya yi wasa da irin su Colorado Rapids, Barnet, Bristol Rovers da Nottingham Forest.

A matakin kasa da kasa, ya buga wa tawagar kasar Ghana wasanni 29, ya kuma ci kwallaye 12.

Ya zura kwallo a minti na 83 a wasan da Ghana ta doke Najeriya da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da karshe na AFCON a shekarar 2008.

Agogo mai shekaru 40 ya rasu ne a ranar 22 ga watan Agustan 2019 bayan ya yi fama da bugun jini tun daga ranar 29 ga watan Janairun 2015.