Mace Za Ta Iya Yin Tafsirin Ramadan A Masallaci?

Tambaya?

Mutane da yawa sun tambaye ni game da hukuncin tara mata a masallaci, mace ta yi musu TAFSIRI da lasifika ?

Amsa;

Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), yana cewa: “Duk lokacin da mutane suka hadu a dakin Allah suna kokarin fahimtar littafin Allah, nutsuwa za ta sauka gare su, kuma Mala’iku za su kewaye su, sannan Allah zai ambace su a wajan wadanda suke tare da shi”.

Muslim hadisi Mai lamba (7030).
Hadisin da ya gabata Yana nuna halaccin mace ta karantar da Alqu’rani a masallaci saboda hadisin bai bambance tsakanin namiji da mace ba.

Sai dai idan mun bi mazhabar malaman da suka inganta hadisin Amru dan Hazm akwai turnuku wajan mace ta yi Tafsiri a watan Azumi, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Yana cewa: “Kar Wanda ya taba Qur’ani sai mai Tsarki” domin Babu yadda za a yi mace lafiyayyiya mai matsakaitan shekaru, ta kammala Ramadhana uku ba ta yi AL:ADA ba.

Malaman Malikiyya suna fifita mace ta yi karatun Sallah a asirce har a sallolin da ake bayyanawa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarci mata da yin tafi idan liman yayi rafkannuwa, idan suna tare da maza don kar aji muryarsu, kamar yadda Bukhari ya rawaito, wannan sai ya nuna ba a son mace ta daga muryarta, to ina kuma ga Lasifikar da za ta isar da sakon ga maza, ga kuma ‘yan social media a gefe wadanda za su yada hotunanta da muryarta a duniya?

Duk da cewa wasu daga cikin mata magabata suna koyar da maza da mata, sai dai ba a bainar Jama’a suke Yi ba cikin daga murya, wannan yasa yin kiyasi akan aikinsu ba zai tafi ba, saboda sababi da illar sun yi hannun riga.

Ayoyi da hadisai da yawa sun nuna halaccin yin wa’azi ga mace, saidai akwai Bambanci tsakanin wa’azi da kuma tafsirin Qur’ani, saboda tafsirin Qur’ani Yana wajabta taba shi yayin nazari da kuma karantarwa, hakan kuma haramun ne ga Mai haila bisa hadisin Amru dan Hazm da ya gabata.

Yana da kyau mata da maza masu yin Tafsiri su yi taka-tsantsan wajan fassara zancen Allah saboda darajar littafin da kuma girman dangantawa Allah abin da mutum ba shi da tabbas.

Ban da tafsirin Alqur’ani akwai hanyoyi da yawa na samun Lada a Ramadhana.

Allah ne Mafi Sani
Dr. Jamilu Zarewa
14/Ramadan 1443.
15/April 2022