Al'umma

Likitoci Sun Ce Sai Anyi Min Tiyata Sannan In Daina Girma – Sulemana

Duk da cewa Sulemana Abdul Samed aka Awuche ya shahara a fadin duniya bayan rahotannin da suka yi na tsawon shi, da kuma yiwuwar kasancewar shi mafi tsayi a duniya, matsala ce a gare shi kuma yana bukatar taimako domin ya daina girma.

Sulemana Abdul Samed aka Awuche,
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Citi TV’s Breakfast Daily a ranar Talata, 10 ga watan Janairu, matashin mai shekaru 29 daga Arewacin Ghana, ya koka da halin da yake ciki, inda ya nemi a taimaka a yi mai magani.

A cewar shi, likitocin asibitin koyarwa na Tamale sun shaida mai cewa zai ci gaba da girma sai dai idan za’a yi mai tiyatar dakatar da shi ba.

“Ina buƙatar taimako don tiyata saboda likitoci sun ce girma yana cikin kai na, don haka ina buƙatar tiyata don dakatar da shi,” Samed ya yi kuka a cikin rahoton Citi TV.

Matashin ya ci gaba da bayyana cewa, shi ma yana fama da matsananciyar ciwo a kashin bayansa, wanda ake iya gani sakamakon tsayin daka.

Baya ga batutuwan da suka shafi lafiya da ke da alaƙa da tsayi, Samed ya koka da yadda zai yi amfani da kayan aƙalla yadi 14 don ɗinka ma kansa tufa ɗaya wanda kuma hakan yana da tasiri a kansa.

Ya yi bayanin yadda sana’ar sa ta kudi ta wayar salula wadda ta zama hanyar samun kudin shiga a gare shi ta durkushe sakamakon matsin tattalin arziki.

“Baya ga tufafi, Awuche ba shi da gadon da ya dace.

“An hada katifarsa mai girman biyu da katifar dalibi don ba shi ta’aziyya, duk da haka, sai ya kwana ta hanyar diagonal.

“Daga nesa ya yi tsayi kuma kamar kato amma idan aka yi la’akari da shi za a ga Awuche ba shi da lafiya a jiki.

“Yana fama da munanan raunuka da bandeji da aka daure a kafarsa ta hagu. Haka kuma akwai raunin da ake iya gani a kafar dama da sauran yanayin lafiya,” in ji citinewsroom.com.

Awuche ya ziyarci wani asibiti a kwanan baya domin duba lafiyarsa da ya saba yi inda aka shaida masa cewa tsayinsa ya kai 9ft 6in (2.89m) tsayin da zai sa ya zama mutum mafi tsayi a duniya.

Sai dai kuma, ya nuna cewa cibiyar kiwon lafiya ba ta da kayan aikin da ya dace, don haka tsayin daka bai yi daidai ba.

Daga baya, wakilin BBC ya auna shi, ya same shi da tsawon kafa 7 4. Idan da gaske dan kasar Habasha yana da 7ft 4.6in, to hakan ya sa ya fi Sulemana Abdul Samed tsayi.