Al'umma

Labarin Hikima: Komai Kayi Kanka Ka Yiwa

Akwai wani mahaukaci yana bara duk abinda ka ba shi sadaka sai yace
“ka yiwa kan ka. Ranar wata kasuwa ya shiga kasuwar domin yin bara, A cikin kasuwar akwai wata mata wacce ke jin haushin wannan Kalmar da wannan mahaukacin ke fada”.

Rana ya sake dawowa kasuwar bara, matar mai jin haushin shi ta kira shi ta ba shi sadakar abinci, bai sani ba ta saka guba a ciki, yana karba ya ce”kin yiwa kan ki”.

Bayan ya juya yayi tafiyar shi, kawai matar ta fashe da dariya ta ce daga
yau ba zaka sake cewa wani ya yiwa kan shi ba.

Yana isa inda yake zama domin cin
abinda ya samo daka bara, kawai
sai ga wasu yara sun taso daga
makaranta, sai suka ce da
mahaukacin, ka yiwa kan ka yau me ka samo ne ka bamu, sai ya ce ba
komai sai wani abinci ga shi ku ci. Suka karba suna murna ya ce da su
idan kun gama ku kai kwanon cikin
kasuwa.

Bayan sun gama, daya daga cikin su ya ce ai wannan kwanon
kamar na maman mu, suka ce eh,
shi ne, sai suka nufi kasuwa matar na ganin su da kwanon ta ce a ina kuka samu kwanon cikin sauri, sai suka ce kin yiwa kan ki ne ya ba mu abinci muka ci kawai matar ta fara kuka, tana cewa lallai na yiwa kai na.

Ƴan uwar mu tuna duk abinda za mu yi mai kyau da mara kyau kan mu muke yiwa, domin haka idan ka turawa ma wani wannan
sako kaima ka yiwa kan ka, mu dai mun tura muku, mun yiwa kan mu.

Allah ya ba mu ikon yiwa kan mu alkhairi.