Labarai

Kungiyar Ƙwadago Ta Amince Da N70,000 A Matsayin Ƙaramin Albashi

Shugabannin kungiyoyin da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC sun tabbatar da amincewa da mafi karancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Bola Tinubu ta kayyade.

Da yake jawabi bayan wani muhimmin taro a fadar shugaban kasa a Abuja, Comrade Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC, ya bayyana matakin da kungiyoyin suka dauka na karbar tayin.

A gefen Comrade Festus Usifo, shugaban TUC, da sauran wakilan ma’aikatan Najeriya, Ajaero ya nuna cewa kungiyoyin sun amince da wannan tayin ne saboda karin kwarin gwiwa da aka bayar.

Ya kara da cewa wani muhimmin al’amari a matakin da suka dauka shi ne alkawarin da shugaban kasar ya yi na sake duba mafi karancin albashi duk bayan shekaru uku, saɓanin shekara biyar da aka sani a baya.

Da farko dai shugabannin kwadagon sun bukaci a biya mafi karancin albashin da bai gaza N250,000 ba. Sai dai kudaden da aka amince da su tare da alkawarin yin bitar lokaci-lokaci ya sa kungiyoyin suka amince da tayin N70,000.