Al'umma

Kisan Abubakar Tafawa Balewa Shi Ya Jefa Najeriya Bala’in Da Take Ciki – Ayodele

A wani rahoto da jaridar Daily Post ta buga, wanda ya kafa Cocin Inri Evangelical Spritual, Primate Elijah Ayodele yace Najeriya za ta cigaba da zama a kiki-kaka idan ba a sauya la’antar da ke kan kasar ba bisa kashe Tafawa Balewa ba.

Idan dai za a iya tunawa Tafawa Balewa shi ne Fira Minista na farko a Najeriya, amma abin takaici wasu sojoji ne suka kashe dan siyasar a ranar 15 ga watan Janairun 1966.

A cikin sanarwar da Oluwatosin Osho ya fitar, mai magana da yawunsa, Primate Ayodele yayi nuni da cewa dole ne ‘yan Najeriya su nemo hanyar da za su kawar da tsinuwar mutuwar Tafawa Balewa da aka yiwa Najeriya kafin kasar ta cigaba.

Hoto: Abubakar Tafawa Balewa.

Sanarwa a wani bangare tana cewa: “Tafawa Balewa ne ya jawo matsalolin Najeriya, ba FESTAC ba ne, idan ba su kawar da la’anar akan Tafawa Balewa ba, to har yanzu Najeriya ta tsaya cik.”

Wannan dai ba shi ne karon farko da Primate Ayodele ya yi magana kan tsinuwar dalilin kashe Tafawa Balewa ba. A wani lokaci a watan Yunin 2022, ya bayyana cewa, duk kashe-kashen da ake yi a kasar nan a hannun mayakan Boko Haram, sakamakon la’ana ne bisa kashe Tafawa Balew. Yace mutuwar Balewa ce ta sanya Najeriya ke fuskantar kalubale na tattalin arziki da siyasa.