Addini
Kasar Da Tafi Kowace Kasa Yawan Musulmi A Duniya
Musulmai mabiya addinin Musulunci ne, wadanda suka yi imani da koyarwar annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, kuma suka rayu akai.
Akwai Musulmi sama da biliyan biyu a duniya, wanda hakan yasa Musulunci ya zama addini na biyu mafi girma a duniya, Kiristanci ne kawai ya wuce musulunci yawan mabiya. Hasali ma, masu bincike da yawa sun yi hasashen cewa musulmi za su fi kiristoci yawa nan da shekara ta 2050.
Kasar da ke yawan mafi yawan al’ummar musulmi a duniya ita ce kasar Indonesiya, kasar tana da kashi 12.7% na Musulman kaf din duniya, sai Pakistan a matsayi na biyu da (11.1%), Indiya ta uku da kashi (10.9%) sai Bangladesh da kashi (9.2%).
- Indonesia (231,000,000)
- Pakistan (212,300,000)
- India (200,000,000)
- Bangladesh (153,700,000)
Kusan kashi 20% na Musulman duniya suna zaune ne a kasashen Larabawa.