Al'umma

Kasar Da Ta Haramta Musulunci Da Masallatai A Cikin Ta

Ka taba mamakin wace kasa ce ke da tsauraran dokoki ga Musulunci, kar ka sake tunani, kasar Slovakia ce.

Kasar da ke tsakiyar Turai ta mayar da Musulunci addinin da ba a san shi ba tun shekara ta 2016.

Dokar da aka yi a waccan shekarar ta tabbatar da cewa Musulmi ba za su iya gina masallatai ba saboda kasar ba ta amince da su ba.

Rahotanni sun nunar da cewa akwai musulmi masu yin ibada kusan 5000 a kasar, amma ba su da masallacin da za su yi ibada, idan har suna son yin ibada, sai su yi hayan dakunan da babu kowa.

Kasar dai kasa ce ta kiristoci, inda mabiya darikar Roman Katolika ke da rinjaye a wurin.