Wasanni
Ɗan Kwallon Kafar Da Ya Taɓa Rasa Bugun Finareti 3 A Wasa Ɗaya
Tsohon dan wasan Argentina Martin Palermo ne dan wasa daya tilo da ya taɓa bugun fanareti uku a wasa daya.
Hakan ya faru ne a wasan Copa America a shekarar 1999 tsakanin Argentina da Colombia.
Fenariti na farko ya bugi post ya dawo, bugu na yayi sama, sannan mai tsaron gida Miguel Calero tare bugu na uku. Colombia ta yi nasara a kan wasan da ci 3-0.
A matakin kulob, Palermo ya taka leda ne a Boca Juniors kuma shi ne wanda ya fi kowa zura kwallaye a kulob din da jimillar kwallaye 236.
A halin yanzu shi ne kocin Aldosivi, wani kulob da ke Argentina.