Siyasa

Jigon PDP A Nasarawa, Haladu Akwashiki Ya Koma APC

Haladu Akwashiki, jigo a jam’iyyar PDP, kuma mai kula da harkokin kwallon kafa a jihar Nasarawa, ya yanke hulda da jam’iyyar PDP a hukumance, ya kuma rungumi jam’iyyar APC mai mulki.

Akwashiki, a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Janairu, ya bayyana kyawawan halaye na shugabancin jam’iyyar APC a dukkan matakai a matsayin dalilin da yasa ya yanke shawarar sauya sheka.

Wasikar dai tana zuwa ne ga Shugaban Jam’iyyar APC a Unguwar sa ta Nassarawa Eggon, a Karamar Hukumar Nasarawa Eggon.

Akwashiki yayi alkawarin yin biyayya ga shugabancin jam’iyyar APC.

A cikin wasikar ya bayar da tabbacin bayar da gudunmuwar kason sa ga ci gaban jam’iyyar APC a kowane mataki na mulki.