Al'umma

Jana’izar Sheikh Abubakar Gero Argungu

Shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS) na kasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, na sanar da lokacin sallar jana’izar Marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda Allah yayi ma rasuwa da yammacin yau (6/9/2023) Laraba bayan fama da gajeruwar jinya.

Za’a gudanar da sallar jana’izar da misalin karfe biyu na rana (2pm) go Alhamis (7/9/2023), a masallacin Idin Sarki dake garin Argungu a jahar kebbi, Naijeriya.

Muna addu’ar Allah ya jikan shi, ya gafarta ma shi, ya sanya Aljanna ta zamo makoma a gare shi. Mu kuma ya kyautata ta mu idan ajalin mu yazo.

إن لله ما أخذ وله ما أعطى وكل شيء عنده بأجل مسمى

Sheikh Kabir Haruna Gombe ya sanar da wannan sanarwar a shafin shi na Facebook.