Al'umma

Jana’iza: Allah Ya Yiwa Sheikh Abubakar Gero Argungu Rasuwa

Assalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wabarakatuhu, yan uwa masu albarka, barkan ku da isowa wannan shafin mai albarka.

Kamar yadda kowa ya sani cewa Allah ya yiwa Sheikh Abubakar Gero Argungu rasuwa a ranar Laraba 6/9/2023, kuma a yau Alhamis 7/9/2023 aka gudanar jana’izar shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ya ku yan masu imani, hakika wannan rayuwa mai karewa ce, kuma dakkan mu zamu koma kamar yadda mutanen da ke gabanin mu suka koma ga Ubangiji. Saboda haka, ya kai dan uwa, ka yiwa kan tanadi domin kyakkyawan karshe da koma makoma mai kyau a gobe kiyama.

Sanin kowa ne cewa Sheikh Gero sanannen malami ne a Najeriya da ma Afrika baki ɗaya, malam yana da mabiya da dalibai wadanda shi kan shi bai san su ba, kuma duk wannan darajar ta samu ga malam ne akan tsayin daka da yayi akan littafin Allah da sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), kuma ya koma ga Allah yana akan su.

Ya ku yan uwa, mu koma ga Allah, kuma mu tuba gare shi tare da yawan istigfari dare da rana, sai Allah ya gafarta muna.

Hakika duba da dandazon mutanen da suka halarci jana’izar Sheikh Gero cikin Najeriya da wajen ta, muna kyatata wa malam zaton cewa ya gama da duniya lafiya, kuma muna addu’ar Allah ya jikan malam, kuma ya yafe masa kura-kuransa.