Al'umma

Iyaka Mafi Kusa Dake Tsakanin Najeriya Da Nijar

Kasashen Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun yi iyaka da juna a arewacin Najeriya, kuma anan ganin wannan iyakar itace mafi kusa da aka taɓa gani da ta haɗa kasashe biyu.

Kusancin wannan iyakar ya ishi mutum yin takun kafa kaɗan kawai domin shiga cikin wadannan kasashen biyu ta iyakar, ba tare shiga jirgin sama ko mota ba.

Haka zalika, mutane zasu yi magana da juna da baki lokacin da daya yana a Najeriya yayin da wani yake a jamhuriyar Nijar.

Wannan iyakar da ta haɗa kasashen biyu tana a kauyen Dole-Kaina da ke jihar Kebbi, kamar yadda kuke iya gani cikin hoton dake a sama.

Shin kun taba ganin wasu iyakoki tsakanin Najeriya da wata kasa da tafi kusa da wannan?