Addini

Hukuncin Wanda Ya Ƙi Karɓar Hadisin Manzon Allah Ingantacce

Sunnar Annabi ita ce madogara ta biyu ta shari’ar Musulunci. Wahayi ya sauka ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Sunna kamar yadda ta zo masa da Alkur’ani.

Hujjar hakan kuwa ita ce fadin Allah madaukakin sarki:

“Kuma ba ya magana a kan son zuciyarsa.
Shi dai wahayi ne da aka saukar."

[Sura: An-Najm 53:3-4].

Allah Ta’ala Ya hore wa Muminai cikakkar sallamawa ga fadin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da hadisan Shi da hukunce-hukuncenSa, gwargwadon yadda Allah Madaukakin Sarki ya rantse da cewa duk wanda ya ji maganar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), sannan ya kafirta da su, bai karbe ta ba, to ba shi da wata alaka da imani ko kadan.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:

“A’a, Na rantse da Ubangijinka, ba za su yi imani ba, har sai sun sanya ka (Ya Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam)) mai hukunci a cikin duk wani saɓani da ke tsakaninsu, kuma ba su sami wani shakku a cikin zukatansu ba, a kan hukuncinka. karɓe (su) cikakku sallama."

[Sura: Nisa’i 4:65].

Don haka ne aka samu ijma’i a wajen malamai cewa duk wanda ya musanta cewa Sunna ta zama hujjar shari’a gaba daya, ko kuma ya karyata hadisin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) – kuma ya san cewa fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) – kafiri ne, wanda bai kai ko da mafi kankantar matakin Musulunci da mika wuya ga Allah da Manzonsa ba.

Imam Is-haaq bn Raahawayh (rahimahullah) yana cewa:

Duk wanda ya ji labari daga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) cewa ya yarda da su in ba wata bazarana, amma sai ya yi watsi da su, ba ta hanyar qyama ba, ko an yi masa barazana (lokacin da ba shi da wani zaɓi) to ya kafirta.

Allah ne mafi sani!