Addini

Hukuncin Shan Rubuta A Musulunci

Tambaya?

Assalamu alaikum malam inada tambaya da Allah menene hukuncin shan rubutu irin Wanda ake rubuta wasu ayoyi sai a wanke a sha.

Amsa;

Wa’alaikumus salam, to malam ba’a samu hakan daga Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba).

Haka nan sahabban shi, sai dai an rawaito halaccin hakan daga wasu daga cikin sahabbai kamar Ibnu Abbas, yazo a Zadul-ma’ad “Ibnu Abbas yayi umarni a rubutawa wata mace mai tsananin nakuda wasu ayoyi na Alqur’ani, don ta samu sauki”.

Haka kuma an rawaito halaccin hakan daga wasu tabi’ai kamar Mujahid, wannan kuma shi ne maganar Imamu Ahmad.

Don haka mutum ya karanta ayoyin shi ne ya fi, domin shi ne ya tabbata a ingantattun hadisai, saidai wanda ya rubuta ya sha ba za’a aibanta shi ba, tun da yana da magabata.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba: Zadul ma’ad 4\170 da Majmu’ul fataawaa 19\64.

02/12/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.