Al'umma

Yadda Ƴan Kungiyar Boko Haram Suka Yi Sallar Idi A Fili

Kungiyar da ke samun goyon bayan kungiyar Boko Haram, ISWAP, wadda a da ake kira Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, ta fitar da hotunan yan ta’addan na kungiyar dake gudanar da Sallar Eid-el-Fitr a wurare daban-daban a Najeriya.

An gudanar da Sallar Eid-el-Fitr ne da akasarin musulmin duniya suka gudanar a ranar 2 ga watan Mayu.

Wasu daga cikin hotunan da SaharaReporters ta gani, an ga maharan na kungiyoyi daban-daban suna salla tare a fili.

A cikin hotunan, an kuma ga kananan yara suna salla tare da ubannin su.

Rundunar sojin Najeriya ta sha yin ikirarin cewa maharan na amfani da yara a matsayin garkuwar mutane da kuma sojan yara a yunkurin su na raunana ayyukan soji.

ISWAP ta shahara wajen fitar da irin wadannan hotuna yayin bukukuwan Sallah.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita domin tunawa da sallar Eid-el-Fitr, inda ya ce gwamnatinsa ta rage karfin Boko Haram.