Al'umma

Hajara: Yarinyar Da Ta Zo Ta Daya A Gasar Karatun Alkur’ani Ta Duniya

Wannan yarinyar suna Hajara Ibrahim, kuma mun samu labarin cewa ita ce daliba mace da tazo ta daya a gasar karatun Alkur’ani mai girma ta duniya, 2024.

Haka zalika, kuma mun samu labarin har an karrama wannan yarinyar da manyan kyaututtuka da suka hada da kyautar kujerun aikin hajjin bana guda uku ita ɗaya mahaifin ta daya Mahaifiyar ta ɗaya kowanen su.

Hafizah Hajara daliba ce a Jami’ar Jihar Gombe. Tana karatun Botany a matakin digiri 200. Ta doke sauran ’yan takara 40 daga kasashe 38 inda ta samu matsayi na farko