Addini

Illolin Da Cikin Kaɗaitar Mace Da Namiji Waɗanda Ba Muharraima Ba

Itade kaɗaita da ƴa mace se kai sai ita wacce ba matar ka ba kuma akwai aure tsakanin ku da ita abune me hadari a addinin musulunci. Wannan ce tasa fiyayyen me ƙaunar mu ɗan gata Allah wanda ba’a taɓa kamar shi ba kuma ba za’a yi ba Annabi Muhammad (ﷺ) yace: “kada wani mutum ya kaɗaita da mace se tare da muharramin ta, wato wanda babu aure a tsakanin su” Imamul Muslim ne da Bukari suka rawaito Hadisin. Wanda aka karɓoshi daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhuma).

Wajibi ne mubi umarni na Annabi (ﷺ) kadda mace da namiji su keɓe a yanayin zance na zawarawan mu ko ƴan matanmu da ke gidajen mu ko duk wata mu’amala da tasa se namiji da mace sun haɗu don kaucewa afkuwar zina.

Mu Sani dukkan zinar da take faruwa idan kabi a hankali za ka ga bata faruwa se da Namiji da mace suka keɓe a inda babu me ganin su.

Daga: Malam Ɗayyabu Umar Memai Rano.