Addini

Fatawar Rabon Gado A Musulunci – Mallam Jamilu Zarewa

Tambaya?
Assalamu alaikum. Dr. Mallam Jamilu Zarewa Mutum ne ya rasu ba shi da kowa sai mahaifiya da ‘yan’uwansa li’abbai, ya gadonsa zai kasance? Daga Hadejia.

Amsa.
Wa’alaikum assalam.
Za’a bawa Uwa kashi daya cikin shida, ragowar kashi biyar din sai a bawa li’abbai duk namiji ya dau Rabon mata biyu.

Allah ne mafi Sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

O2/02/2022