Al'umma

Sabon Shugaban Kungiyar Boko Haram

Hotunan na baya-bayan nan na Bakoura Buduma, shugaban kungiyar Boko Haram na yanzu sun bayyana a yanar gizo, a yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin ‘yan kungiyar masu jihadi da ake kira ISWAP da Boko Haram a dajin Sambisa.

Bakoura Buduma, wanda aka fi sani da Bakoura Doro, ko kuma Abou Oumaymah, ya zama shugaban Boko Haram bayan mutuwar Shekau Abubakar.

Bakoura Doro, ko kuma Abou Oumaymah da ya karbi ragamar shugabancin kungiyar ta Boko Haram, shi ne ke jagorantar kazamin fadan da ake yi da kungiyar IS a yankin yammacin Afirka a cikin ‘yan watannin da suka gabata a cewar wani masani kan yaki da ‘yan ta’addan mai suna Zagazola Makama.

Idan dai za a iya tunawa kungiyar Boko Haram da kungiyar IS a yankin yammacin Afirka na fama da rigingimun da ba a warware su ba wanda ya yi nasarar kashe mayakan Jihadi da dama a cikin kungiyoyin.

An kuma kashe Shakau Abubakar bayan wani harin bazata da kungiyar IS ta kai a yankin yammacin Afirka (ISWAP) a sansanonin Boko Haram da ke kusa da tafkin Chadi a arewa maso gabashin Najeriya.