Al'umma

Dr. Zakir Naik A Sakkwato: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani

Takaitaccen abin da ya faru kafin zuwan Dr. Zakir Naik Sakkwato da kuma bayan zuwan shi.

Mai alfarma Sarkin Musulmi (Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III) ya shafe shekaru da dama yana neman Dr. Zakir Naik yazo jihar Sakkwato domin ya gabatar da darasi a birnin Sokoto. Amma sai a wannan karon Allah ya ƙaddara Dr. Zakir Naik ya samu karbar gayyatar Sarkin Musulmi.

Duba cewa idan Dr. Zakir Naik yazo Najeriya za’a samu mabiya addinin Kirista sosai da zasu sauya daga kafirci zuwa addinin Muslunci.

Kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN ta shirya munafurci sosai don ganin cewa gwamnatin Tarayyar Najeriya ta hana Dr. Zakir Naik shigowa a Najeriya ta hanyar dalilan sharri kamar haka:

  1. Babu tsaro a Najeriya, saboda haka kasa Dr. Zakir Naik yazo har sai an samu kwanciyar hankali.
  2. Kungiyar CAN ta ce zuwan Dr. Zakir Naik Najeriya zai haifar da rikicin addini tsakanin Musulmi da Kirista, saboda haka gwamnatin Najeriya ta dakatar da wannan gayyatar.
  3. Bayan Dr. Zakir Naik da tawagar shi sun sauka a Sakkwato, kungiyar CAN ta nemi Sarkin Musulmi ya bada hakuri na gayyatar malamin addinin ba tare da bin dokoki ba.

A tunanin kungiyar CAN ya kamata Sarkin Musulmi ya nemi izinin gwamnati da izinin rundunonin tsaro cewa yana son gayyatar Dr. Zakir Naik zuwa Sakkwato, Najeriya.

Wannan yasa mai Alfarma Sarkin Musulmi ya fito ya bayyana cewa:

Ba zan ba kowa hakuri ba akan wannan gayyatar, kuma zan ci gaba da gayyato Dr. Zakir Naik domin gabatar da darussa masu muhimmanci acikin addinin muslunci.

Bayan Haka

Sai wasu malamai dake cikin gida yan son zuciya da hassada suka ce:

Dr zakir Naik ba dan kungiyar IZALA ba ne, ba dan DARIKA ba ne, ba dan SHI’A ba ne, ba dan SALAFIYYA ba ne, Dr. Zakir Naik baya da wata kungiyar addini.

Abin Sani

Dr. Zakir Naik malami ne mai koyar da Alqur’ani da Sunnar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).

Babban burin shi shine mutane su fahimci addinin Musulunci.

Saboda son zuciya malamman mu da yawa basuji dadin zuwan wannan bawan Allah ba. Har wasu ke turawa Sarkin Musulmi sakonnin SMS da kalamai na son zuciya da rashin adalci saboda ƙiyayya da gaskiya.